Connect with us

Labarai

Shugaban Majalisar wakilai ya buƙaci ministoci da masu riƙe da muƙaman siyasa su bayyana ayyukan da suka gudanar

Published

on

Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya, Tajuddeen Abbas, ya buƙaci ministoci da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa a gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da su bayyana ayyukan da suka gudanar, ya na mai cewa nuna biyayya ga shugaban ƙasa ba tare da ayyukan da za a iya gani ba, ba zai ƙara gamsar da ’yan kasa ba.

Tajuddeen Abbas, ya bayyana hakan ne a Abuja, inda ya sanar da shirin ƙirƙirar tsarin tattara bayanan ayyukan gwamnati mai suna PBAT Stewardship Account.

Ya buƙaci masu riƙe da muƙaman siyasa su gabatar da rahoton ayyukansu cikin kwanaki 90, tare da bai wa al’umma damar tantance ayyukan da aka gudanar.

Ya kuma bayyana cewa shi da kansa zai gabatar da rahoton ayyukan da ya taimaka aka gudanar a mazaɓarsa ta Zariya, Jihar Kaduna, Arewa maso Yamma da Najeriya baki ɗaya cikin kwanaki 14.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!