Labarai
Katsina: Yan sanda sun kama mutanen da ake zargi da yi wa yan bindiga safarar makamai

Rundunar yan sandan Jihar Katsina ta kama wasu da ake zargi da yi wa ’yan ta’adda safarar makamai, inda aka kwato babbar bindiga da harsasai sama da guda dubu daya.
Wannan na cikin wata sanarwa da Kwamishinan Tsaro da Harkokin cikin gida na jihar Katsina, Dakta Nasir Mu’azu, ya fitar a Litinin din makon nan.
Sanarwar ta bayyana cewa, jami’an ƴan sanda daga garin Ingawa ne suka tare wata mota kirar Golf da ake yin amfani da ita wajen jigilar makaman a kan hanyar Ingawa zuwa karkarku, inda aka cafke mutane biyu da ake zargi, Abdulsalam Muhammad mai shekaru 25 da Aminu Mamman mai kimanin shekaru 23, dukkansu mazauna Ƙaramar Hukumar Safana.
Sanarwar ta kara da cewa, makaman da aka kwato sun hada da babbar bindiga da harsasai 1,063 na bindiga kirar AK-47.
Gwamnatin Jihar Katsina ta yaba da ƙoƙarin ’yan sanda, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da tallafa musu wajen yakar ta’addanci da sauran manyan laifuka.
You must be logged in to post a comment Login