Connect with us

Labarai

Mun cafke masu safarar makamai a Katsina – ‘Yan sanda

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce ta samu nasarar cafke wasu da ake zargi da safarar makamai a jihar.

Kwamishinan ’yan sandan jihar Sunusi Buba Sunusi ne ya bayyana hakan ga manema labarai yau a shelkwatar ‘yan sandan jihar Katsina.

Sunusi Buba ya ce rundunar ta dade tana neman Lawan Zayyana mai shekaru 35 dake Kauyen Muduru a karamar hukumar Mani, wanda ake zargi da safarar makamai ga ‘yan bindiga a jihar ta Katsina.

Kwamishinan ya ce cikin abubuwan da aka samu a hannunsa sun hada da bindigogi da alburisai guda 170 masu harbo jiragen yaki da sauran su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!