Labarai
Kebbi: Lakurawa sun hana manoma sayar da dabbobi don siyan injinan Noma

Rahotonni daga jihar Kebbi, sun tabbatar da cewar ‘yan ta’addar Lakurawa sun shiga garuruwa fiye da 10 a ƙaramar hukumar Augie ta jihar inda suka gargaɗi jama’a da ka da su ƙara sayar da shanunsu domin sayan injinan huɗa da ke amfani da Man fetur.
Ta cikin wasu bayanan sirri da wani mazaunin yankin ya fitar, ya shaida cewa suna sayar da shanun ne domin su sayi motar noman shinkafa amma a yanzu basu da iko sai dai su hakura domin su tsira da rayukan su, sakamakon barazana da suke fuskanta daga ‘Yan ta’addar.
Shaidun gani da ido a yankin na Augie sun ce Lakurawan kan shiga gari a kan Babura, dauke da bindigu kuma sukan kwashe dabbobi a cewar ‘yan garin da suka nemi a sakaye sunansu.
Yanzu haka dai ana ci gaba da zaman dar-dar a yankin, yayin da jama’a ke roƙon gwamnati da hukumomin tsaro su tashi tsaye domin kawo ƙarshen wannan matsala da ta dabaibaye rayuwar su da amfanin gonakin su.
You must be logged in to post a comment Login