Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kannywood sun buƙaci shugaban ƙasa ya tabbatar da anyi adalci a shari’ar gwamnan Kano

Published

on

Wasu daga cikin jarumai a masana’antar Kannywood sunyi kira ga shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu da ma’aikatar Shari’a ta ƙasa da su tabbatar da cewa anyi adalci a hukuncin zaben gwamnan Kano da kotun koli zatayi

Shugaban ƙungiyar ƴan Kannywood magoya bayan gwamnan kano Sani Musa Danja ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudana a ranar Asabar 09 ga watan Nuwamba 2023 inda yayi kira da cewar shugaban kasa mutum ne mai mutunta kundin tsarin mulkin ƙasar nan.

“Sani Danja Ya kara da cewar al’ummar jihar Kano sun fito sun zabi gwamnan Abba Kabir Yusuf da kuri’u mafi rinjaye kamar yadda hukumar zabe ta tabbatar dashi, sai dai wasu kotuna na neman soke nasarar da al’ummar jihar kano suka samu.

Haka kuma sun buƙaci ayi duba da masalahar al’ummar jihar Kano domin ganin an tabbatar musu da zaɓin su na abin da suka za ɓa.

Kazalika in akayi duba da irin abubuwan da gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf yake yi na aikace-aikace abin a yaba ne kuma abine da zai samarwa da jihar kano ci gaba a fannoni daban daban.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!