Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ketare-Koriya ta kudu zata rattaba hannu kan yarjejeniya da kasashen Afrika

Published

on

Koriya ta Kudu na shirin rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya da kasashen Afirka 8 domin taimaka musu inganta harkokin noman shinkafa da ma kaucewa dogaro da shigar da kayayakin abinci daga ketare.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ne ya bayyana hakan, bayan wata sanarwar ta ministan noma na kasar, wanda ke zuwa a daidai lokacin da nahiyar ke fuskantar barazana ta karancin abinci.

Karkashin wannan shiri, Koriya ta kudu za ta samar da manyan gonakai a kasashen Ghana da Gini da Gini Bissau da Gambiya da Senegal da Kamaru da Yuganda gami da kuma Kenya domin samar da wani sabon nau’i na shinkafa.

Sama da dalar Amurka miliyan 77 ne wannan shirin samar da shinkafa a kasashen na Afirka zai lakume nan da shekaru 4 da ke tafe.

Rahoton: Abdulkadir Haladu Kiyawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!