Ƙetare
Ketare: Sama da mutane miliyan uku ne zasu kada kuri’a a zaben kasar Saliyo
Fiye da mutune miliyan uku ne ake sa ran za su kada kuri’a domin zaɓen shugaban kasa da ‘yan majalisar dokoki da kuma na kananan hukumomi, a Kasar Saliyo.
Wannan dai shi ne zaɓe na biyar tun bayan kawo karshen yaƙin basasar kasar wato shekaru 21 da suka gabata.
Shugaba Julius Maada Bio da ke neman sake tsayawa na tsawon shekaru biyar, zai fatata ne da wasu ‘yan takara 12, amma masana sun ce babban abokin hamayyarsa shi ne Dr Samura Kamara, wanda ya zo na biyu a zaɓen shugaban kasar da aka yi a 2018.
Rahoto: Ahmad Kabo Idris
You must be logged in to post a comment Login