Ƙetare
Ketare: Za’a Bude mashigar Rafa don kai agaji: Baden

Shugaban kasar Amurka Joe Biden, yace Shugaban Masar Abdel Fattah Al-Sisi ya amince da bude mashigar Rafah ga wasu manyan motoci dake dauke da kayan agaji zuwa Zirin Gaza.
Biden din ya bayyana hakan ne da yake jawabi a cikin jirgin saman Air Force One yayin wata ziyarar bazata ga manema labarai a cikin jirgin.
Yana me bayyana cewa Shugaba Sisi ya amince ya bude mashigar Rafah, don bai wa motocin daukar kaya 20 na taimakon kayan jin kai zuwa Gaza.
Rahoton: Sunusu Shu’aibu Musa
You must be logged in to post a comment Login