Kiwon Lafiya
Kimanin mutane 16 suka rasa rayukansu a rikicin jihar Plateau
Rundunar ‘yan-sandan kasar nan ta ce adadin mutanen da suka rasu sakamakon rikice-rikice tsakanin al’umma a Jihar Plateau ya kai 16, sai dai wasu mazauna yankunan da abin ya auku sun ce adadin ya kai 25.
Jaridar Premium Times ta ta wallafa a shafinta na Intanet cewa ko a ranar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci Jihar an samu barkewar rikicin a karamar hukumar Bokkos daga ranar 7 zuwa 9 ga wata.
A jiya Lahadi ne dai Rundunar ‘yan-sandan ta ta bakin kakakinta na Jihar Terna Tyofev ta sanar da cafke wani mutum guda da ake zargi da hannu bayan da aka same shi dauke da bindiga kirar AK47 guda a garin Daffo.
Terna Tyofev ya tabbatar da mutuwar mutum 16 sakamakon hare-hare a wasu yankuna na Jihar ta Plateau daga ranakun 7 zuwa 9 ga watan Maris din nan da mu ke ciki, wanda hakan ya sanya suka tura jami’ansu wuraren domin tabbatar da wanzuwar zama lafiya da doka da oda.
Sai dai shugabannin al’ummar yankin yayin zantawarsu da manema labarai sun shaida cewa mutane 25 ne suka mutu sannan wasu da dama sun bace.
Garuruwan da al’amarin ya faru sun hadar da Dai da Kugul da Hurum da Dahua da Malul da Warren da Joso da Ganda, sauran sune Shilim da Morok da Mandung da dai sauransu.