Labarai
Kisan Ƴar Aiki: An gurfanar da wadda ake zargi a gaban kotu
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce, ta samu hujjoji a kan matar da ake zargi da hallaka ƴar aikinta a Kano.
Mai magana da yawun ƴan sandan Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a.
Kiyawa ya ce, yanzu haka an gurfanar da wadda ake zargin a gaban kotu bisa zargin kisan kai.
Dangane da batun cizon Muzuru ya ce, bincike ya gano cewa Muzuru ya taɓa cizon marigayar tun a baya.
Ya ƙara da cewa, zuwa yanzu sun samu shaidu uku ƙwarara da suka ganewa idon su yadda lamarin ya faru.
You must be logged in to post a comment Login