Labarai
Kishi: Wata mata ta kashe ɗan kishiyar ta a Kano
Rundunar yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama wata mata mai suna Fiddausi Bello mai shekaru 30 bisa laifin sanyawa ɗan kishiyarta guba.
Lamarin dai ya faru a ƙauyen Gainawa a ƙaramar hukumar Kura anan Kano.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan ga Freedom Radio.
Kiyawa ya ce, bayan ta bai wa jaririn guba mai suna “Gamalan A” rai yayi halin sa, tun a ranar 15 ga watan Satumbar da muke ciki.
DSP Abdullahi Kiyawa ya kuma ce, tuni matar ta amsa laifin ta, inda ta ce, ta ɗau matakin ne sakamakon yadda kishiyar ta ta taci amanar ya wajen aure mata miji.
Sai dai ya tabbatar da cewa za a miƙa matar sashin binciken manyan laifukan don faɗaɗa bincike.
You must be logged in to post a comment Login