Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Ko babban Akanta na Najeriya zai yi takarar Gwamnan Kano?

Published

on

Ahmad Idris shine babban akanta na Najeriya, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya nada Alhaji Ahmad Idris a matsayin da yake kai a yanzu.

A shekarar 2015 lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zama shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu ,shugaban kasar yayi sauye sauye a gwamnatin sa musamman ma manyan mukamai na Gwamnatin tarayyar ta Najeriya.

Ofishin babban akanta na kasa ba karamin ofishi ba ne da yake kula da fita da hada hadar kudade a matakin na gwamnatin tarayyar ta Najeriya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ayyana nadin Alhaji Ahmad Idris a watan Yunin shekarar 2015 domin yin wa’adin shekaru hudu a matsayin babban akantan na Najeriya.

Nadin nasa ya zo bayan da Gwamnatin ta shugaban kasa Muhammadu Buhari ke kokarin toshe kafafan da kudade ke zurarewa da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

A ciki kuma har da tsarin nan na asusun bai daya da ake kira da TSA a turance.

A shekaru hudun farko na gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari babban akanta Ahmad Idris yayi bajinta wajen aiwatar da manufofin gwamnatin ta tarayyar Najeriya.

Ana ganin hakan ne yasa bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake lashe zaben shugaban kasa a shekarar 2019 ya sake nada Alhaji Ahmad Idris a matsayin babban akanta na Najeriya domin yin sabon wa’adi.

Sake nadin na Alhaji Ahmad Idris da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ana ganin wata manuniya ce ta irin bajintar da ya nuna a karon farko bayan an nada shi.

Shekarar 2023: Mecece makomar Takai a siyasar Jahar Kano?

Rikicin Gwamnatin Kano da Masarauta: Siyasa ko cigaba?

Sake nadin da shugaba Muhammadu Buhari yayiwa Alhaji Ahmadu Idris ya saka wasu matasa anan jihar Kano da wasu kungiyoyi ta kafofin sadarwa suka yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari game da matakin da ya dauka na sabunta aikin Ahmad Idris.

Shi dai babban Akantan na Najeriya tun samun mukamin nasa yayi shuhura wajen taimakawa matasa musamman ma da suka fito daga nan jihar Kano wajen sama musu aiki a guraben gwamnatin tarayya.

Jim kadan bayan sake nadin nasa a matsayin babban akanta na tarayyar Najeriya kungiyoyi suka rika yin hubbasa wajen karrama shi , musamman ma kungiyoyi da ke cikin birnin Kano da aka sani da Badala wato tantagaryar cikin gari.

Bayan haka ma gidauniyar da ya kafa ta samar da aikin yi ita ma na jan hankali ga  matasan da ke neman dogaro da kai.

Daga cikin guraren da babban Akanta Ahmad Idris ke rayawa har da karamar hukumar Gezawa inda yake gina wata babbar kasuwa a garin na Gezawa.

Baya ga samarwa matasa aikin yi ana ganin Ahmad Idris yayi abubuwa da dama da suka taba rayuwar matasa da sauran su.

Ko bayan dawowar sa karo na biyu a matsayin  babban akanta na Najeriya , yana karbar kungiyoyi da dama domin tallafa musu.

Ta kai akwai wasu kungiyoyi na matasa dake ganin ya kamata babban Akanta na Najeriya ya shiga siyasa a matakin jihar Kano dan bayar da gudunmawar sa wajen cigaban jihar.

Amma masu fashin baki na siyasa na ganin cewa babu wata kujera da Ahmad Idris ya kamata ya nema idan ya fada harkokin siyasa face kujerar gwamnan jihar Kano.

Jagorancin siyasar birnin Kano: Sha’aban Sharada ko Mukhtar Ishaq Yakasai?

A yayin da zaben shekara 2023 da Najeriya zata sake yi kuma a lokacin da wa’adi na biyu na Ahmad Idris zai kare ana ganin  cewa da zai fito takarar gwamnan jihar Kano zai bayar da gudunmawa kwarai da gaske wajen cigban jihar Kano.

 

Ko babban akantan zai amsa kiran jama’a wajen fitowa takarar Gwamna a shekarar 2023.

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!