Connect with us

Manyan Labarai

Rikicin Gwamnatin Kano da Masarauta: Siyasa ko cigaba?

Published

on

YADDA DOKAR KAFA MASARAUTU TA SAMO ASALI

A ranar 8 ga watan Mayu na shekarar 2019 ne Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sa hannu a wata doka da ta bayar da damar kirkirar masarautu guda hudu daga masarautar Kano.

Kamar yadda tsohuwar majalisar ta Jihar Kano ta fada wata kungiya ce ta nemi a kirkiri sababbin masarautun wanda daga baya al’ummar masarautun suka zo majalisar ta dokokin jihar Kano suna masu goyon bayan kudurin majalisar ta jihar Kano na fito da sababbin masarautu.

Jim kadan bayan sakawa dokar kirkiro masarautun Karaye da Rano da Bichi da Gaya hannu Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya zagaya sababbin masarautun domin mika sandar kama Mulki ga sarakunan na Jihar Kano.

Gwamna Ganduje ya kuma tara sababbin Sarakunan a dakin taro na Sani Abacha inda ya mika musu takaddun kama aiki, duk wannan ya faru ne kafin ranar sake rantsar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a karo na biyu.

UMARNIN KOTUNA

A satin da aka fara rabawa sababbin Sarakunan sandar kama aiki ne  babbar Kotun Jihar Kano ta bayar da umarnin dakatar da basu sanda inda wanda ya shigar da karar Rabi’u Gwarzo kuma Dan majalisa mai wakilitar yankin na Gwarzo ya shigar gabanta.

Amma duk da haka sai da gwamnatin ta Jihar Kano ta rabawa sababbin Sarakunan sanda sannan kuma ta cigaba da mu’amala da sauran Sarakunan na Karaye da Rano da Bichi da Gaya.

KIN BIN UMARNIN KOTU.

Bayan kammala rabawa Sarakunan sanda an cigaba da kai gwamnatin jihar Kano kara da ya hada da masu zaban Sarki.

Masu zaban Sarki da suka kai gwamnatin Jihar Kano kara sun hada da Madakin Kano Yusuf Nabahani da Sarkin Bai Mukhtar Adnan da Makaman Kano Sarki Abdullahi Ibrahim sai Sarkin Dawaki mai Tuta Bello Abubakar.

Masu zaban sarkin da suka kai gwamnatin ta jihar Kano kara yankunan su sun fada cikin sababbin masarautun da Gwamna Ganduje ya kirkira.

Kasar Madakin Kano wadda itace Dawakin Tofa ta fado karkashin sabuwar masarautar Bichi yayin da kasar Makaman Kano wato Wudil ta fada masarautar Gaya da kuma kasar Sarkin Dawaki mai Tuta itama ta fada masarautar Gaya, kasar Sarkin Bai ta Dambatta ta fada masarautar Bichi.

A ranar 21 ga watan Nuwamba ne babbar kotun Jihar Kano karkashin Usman Na’abba ta yanke hukunci inda tace sababbin masarautun ba’a yi su bisa ka’ida ba kuma ta rusa su nan take.

Bayan kwanaki Gwamnatin Jihar Kano ta sake mayar da kudurin neman kafa masarautu wanda bayan kwanaki kadan majalisar ta sahale da dokar ,Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sake saka mata hannu.

Ana tsaka da haka ne sai Gwamnatin Jihar Kano ta nada Sarki Muhammadu Sunusi II a matsayin sabon shugaban majalisar Sarakuna ta jihar Kano wanda ya dade bai amsa ba.

Sai da ta kai Gwamnatin Jihar Kano ta sake aikawa da Sarkin na Kano wasika inda ta umarce shi ko ya karbi mukamin shugaban majalisar Sarkunan na Kano ko akasin haka.

ZARGIN SHIGAR SARKIN KANO SIYASA.

Amma masana da masu sharhin al’amuran yau da kullum na alakanta kirkirar masarautu hudu a jihar Kano da siyasa, inda Gwamnatin jihar Kano ke zargin Sarkin Kano da daukar bangaranci lokacin zaben Gwamna na shekarar bana.

Ko a lokacin da hukumar zabe ta ayyana Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan Jihar Kano a watan Maris din da ya gabata, sai da aka cire hoton mai marataba Sarkin Kano daga babban dakin taro na Coronation Hall dake gidan Gwamnati.

Dakin taron na Coronation Hall an gina shi ne musamman a shekarar 2014 domin bawa Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II sandar kamar aiki ,wacce akayi a ranar 7 ga watan Fabrairun Shekarar 2015 lokacin mulkin tsohon Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso.

KIRKIRO SABABBIN MASARAUTU DOMIN CIGABA.

Duk da cewa mukamin Sarki mukami ne na kawa da kuma nuna al’ada da Addini da Tarihi ,Gwamnatin ta Jihar Kano karkashin Jagorancin Dr Abdullahi Umar Ganduje tace ta kirkiri sababbin masarutun ne domin kawo cigaba.

Amma masana al’amuran yau da kullum na ganin kirkirar masarautu ba cigaba zai kawo ba, sai dai rabuwar kai tsakanin al’ummar Jihar Kano baki dayan su wanda masarautun gaba daya ke karkashin jiha daya.

Har yanzu akwai wasu jihohi a arewacin kasar nan da suke da masarautu fiye da daya kamar su Jigawa da Niger da Bauchi da Nassarawa da Borno amma cigaban su bai kai na Jihar Kano ba.

Amma shi kansa Gwamna Abdulllahi Ganduje ya taba cewa zai gina manyan asibitoci a sababbin masarautun na Jihar Kano guda hudu.

Shin wadannan masarautu domin cigaba ne ko akasin haka, lokaci ne kawai zai iya bayyanawa?

 

Labaran Kano

Sarki Sanusi II ya taya Ganduje murnar samun nasara a Kotu

Published

on

Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II, ya taya gwamnan jihar Kano murnar samun nasara a kotun koli na jaddada Kujerar sa a matsayin zababben gwamnan jihar Kano.

Muhammadu Sunusi na II, ya yi wannan kiran ne a yau a dakin taro na Afirka House, a lokacin da ya raka Oba na Benin Omo N’oba N’Edo UkuAkpolokpolo Ewuare na II, ziyara ta musamman wajen gwamnan jihar Kano.

Kazalika, Sakin yayi kira da a samu hadin kai tsakanin masu rike da madafun iko da masu sarautun gargajiya, don samar da jagoranci na gari tare da yiwa al’umma aiyyukan raya kasa.

Har ila yau, Muhammadu Sunusi na II, ya kara da cewa, lokaci ya yi da za’a manta da banbance da rashin jituwa tare da sa cigaban jiha a gaba.

Gwamna Ganduje ya nada Sarkin Kano Muhammad Sunusi shugaban majalisar Sarakunan Jihar Kano

Sarkin Kano ya bude masallacin juma’a na sabuwar jami’ar Bayero

Hukumomin kiwon lafiya na yin dukkanin mai yuwa kan cutar lassa- Sarkin Kano

A nasa jawabin Oba na Benin, Omo N’Oba N’Edo Uku Akpolokpolo Ewuare na II, ya ce Sarakunan gargajiya a fadin kasa na da muhimmiyar rawar da suke takawa wajen hadin kan al’ummar kasar nan mai Kabilu da al’adu daban -daban, wanda hakanne ya sanya ya taso musamman don jaddada wannan kudiri tsakanin al’ummar sa da ta jihar Kano.

Shima a nasa jawabin gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya ce gwamnatin sa a shirye take da hada kai tare da karbar shawarwari, daga dukkan masu rike da masarautun gargajiya a fadin kasar nan, kasancewar su wata Rumfa mai muhimmanci wajen, hadin kan al’umma, da zaman lafiya tare da bunkasa kasa gaba daya.

Wakilinmu na fadar gwamnatin jiha Aminu Halilu Tudunwada, ya ruwaito mana cewa Sarakunan guda biyu na Kano da na Benin, sun samu rakiyar tawagar wasu daga cikin hakimansu a ziyarar da suka kai fadar gwamnatin jiha.

Continue Reading

Labaran Kano

Za’a sake tona wata gawa da aka binne-Ustaz Sarki Yola

Published

on

Babbar kotun shari’ar musulunci karkashin Mai sharia Ustaz Sarki Yola a Kano tayi umarni da a tono wata gawa da aka binne ba daidai ba.

Mai shari’ar Ustza Sarki Yola ya bada umarnin ne bayan zaman kotun a yau Litinin

Ku saurari cikakken labarin cikin shirin Inda rank ana yau tare da Nasiru Salisu Zango da misalin karfe 9 da rabi

 

 

Continue Reading

Labaran Kano

Ya wajaba al’ummar mu su bunkasa tattalin arzikin Kano- Oba Ewuarin

Published

on

Sarkin masauratar al’ummar Benin Oba Ewuarin Ogidigan na biyu ya ja hankalin al’ummar masarautar Edo mazauna Kano da su himmatu wajen kawo  cigaban ta fuskar tattalin arzikin jihar Kano.

Ewuarin Ogidigan ya bayyana hakan ne yayin wani taron al’mmar jihar Edo mazauna jihar Kano a yau.

Ya ce shakka alaka tsakanin jihar Kano da Edo dadaddiya ce,  da ta haifar da alfanu a tsakanin jihohin biyu.

A yayin taron ‘Yan Dakan Kano, Alhaji Abbas Muhammad Dalhatu ne ya wakilci Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu.

Taron al’ummar jihar Edo karkashin masarautar Benin ya samu halartar al’ummar masarautar Benin mazauna jihar Kano,  da sauran ‘yan majalisar Sarkin na Benin.

Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa, Masarautar Benin ta samu asali ne tun shekaru 900 da suka shude,  da yanzu take karkashin jihar Edo.

Galibi dai a wadancan shekaru masarautar tayi sarakuna da suka yi shura a bangarori daban-daban na rayuwar al’umma.

Yankin da sarakunan suke yin shugabanci a baya,  ya kasance mai dinbim tattalin arzikin karkashin kasa da albarkatun noma.

Continue Reading

Now Streaming

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!