Labarai
Ko kaɗan umarnin kotu bai shafi muƙabala ba – Barista Fagge
Lauyan nan Barista Abba Hikima Fagge ya ce, umarnin da kotu ta bayar a ranar Juma’a bai hana gudanar da Muƙabalar malamai ba.
A zantawarsa da Freedom Radio, Barrister Fagge ya ce, odar farko da kotu ta bayar, ta shafi abubuwa guda biyar waɗanda suka haɗa da.
1. Kada Abduljabbar ya ƙara buɗe masallacin sa da ke filin mushe.
2. Kada ya sake yin wa’azi a kafafen yaɗa labarai.
3. Kada kafafen yaɗa labarai su ƙara sanya karatunsa.
4. Jami’an tsaro su tabbatar da cewa an bi waɗannan umarni.
5. Sannan kada wani mai wa’azi ya ƙara yin wata magana da za ta haifar da tunzuri.
Hikima ya ce, wannan shi ne abin da kotu ta faɗa kuma a ciki babu maganar Muƙabala.
Kuma kotu ta bayar da wannan umarnin ne har zuwa kammala bincike, kuma daga cikin hanyoyin binciken shi ne muƙabala.
Karin labarai:
Wata Sabuwa: Malam Abduljabbar ya yi watsi da dakatar da muƙabala
Har yanzu muna nan a kan tuhumar da mu ke yiwa Sheikh Abduljabbar – Malaman Kano
Umarnin kotu na ranar Jumu’a kuwa, Barrister ya ce, ai kotun cewa ta yi a tabbatar an ci gaba da bin wancan umarni saboda haka babu inda kotu ta hana muƙabala.
Mun tuntuɓi Barista Ma’aruf Yakasai wanda shi ne ya nemi kotu ta dakatar da muƙabalar.
Ya kuma ce, ai yin zaman muƙabala ya saɓa da umarnin kotu na hana Malam Abduljabbar ɗin yin karatu.
Ya ce, “Idan aka zauna muƙabala ai an sake bashi dama ya karanto waɗannan abubuwan da ake maganar ya yi su na ba daidai ba kenan”.
Tun daren Juma’a ne Gwamnatin Kano ta fitar da sanarwa ta hannun Kwamishinan yaɗa labarai da a ciki ta ce, ta yi biyayya ga umarnin kotu a don haka babu Muƙabala ranar Lahadi.
You must be logged in to post a comment Login