Kiwon Lafiya
Ko kun san amfanin ɗan itaciyar Kanya a jikin ɗan adam
Ƙwararren likita a fannin cimaka a Aminu Kano ya ce, “Kanya” guda ce daga cikin ƴaƴan itatuwa da ke ɗauke da sinadarin vitamin A da kuma vitamin C.
Dakta Umar Yahuza ya ce, Allah ya halicci tsirrai da bishiyoyi wanda da yawa daga cikinsu suna da matuƙar amfani a jikin mutum.
“Mafi yawan tsirrai da ƴaƴan itatuwa suna ɗauke da magunguna da kuma bai wa jiki abin da ke buƙata ko da kuwa itatuwan da suke bada iska ne”.
“A jikin “Kanya” akwai sinadarin da yake ƙara ƙarfin jiki da jijiya wato “Culcium” akwai kuma sinadarin “Manganise” wanda shi kuma sinadari ne da yake da ƙaranci a cikin abincin da aka fi ci yau da kullum”.
“Kanyar dai na ɗauke da sindarin Vitamin A da kuma Vitamin C da kuma “Fyber” wanda sinadari ne da yake hana yin bayan gida mai tauri matukar ba ƙwallayen ta mutum ya haɗeyi ba”.
Likitan ya ci gaba da bayani kan muhimmancin “Kanya” kamar haka “Fatar ta ma na ɗauke da sinadarin “Fyber” wanda yake da matuƙar amfani a jikin mutum kodan ƙarin lafiya.
A cewar likitan dukkanin wani nau’in ƴaƴan itatuwa da suka zo suna ɗauke da sinadarin da jikin ɗan adam ke buƙata a wannan lokaci, har ma ya ce yana da matuƙar muhimmanci a riƙa saye ana ci don inganta lafiya.
You must be logged in to post a comment Login