Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Ko kun san amfanin ɗan itaciyar Kanya a jikin ɗan adam

Published

on

Ƙwararren likita a fannin cimaka a Aminu Kano ya ce, “Kanya” guda ce daga cikin ƴaƴan itatuwa da ke ɗauke da sinadarin vitamin A da kuma vitamin C.

Dakta Umar Yahuza ya ce, Allah ya halicci tsirrai da bishiyoyi wanda da yawa daga cikinsu suna da matuƙar amfani a jikin mutum.

“Mafi yawan tsirrai da ƴaƴan itatuwa suna ɗauke da magunguna da kuma bai wa jiki abin da ke buƙata ko da kuwa itatuwan da suke bada iska ne”.

“A jikin “Kanya” akwai sinadarin da yake ƙara ƙarfin jiki da jijiya wato “Culcium” akwai kuma sinadarin “Manganise” wanda shi kuma sinadari ne  da yake da ƙaranci a cikin abincin da aka fi ci yau da kullum”.

“Kanyar dai na ɗauke da sindarin Vitamin A da kuma Vitamin C da kuma “Fyber” wanda sinadari ne da yake hana yin bayan gida mai tauri matukar ba ƙwallayen ta mutum ya haɗeyi ba”.

Likitan ya ci gaba da bayani kan muhimmancin “Kanya” kamar haka “Fatar ta ma na ɗauke da sinadarin “Fyber” wanda yake da matuƙar amfani a jikin mutum kodan ƙarin lafiya.

A cewar likitan dukkanin wani nau’in ƴaƴan itatuwa da suka zo suna ɗauke da sinadarin da jikin ɗan adam ke buƙata a wannan lokaci, har ma ya ce yana da matuƙar muhimmanci a riƙa saye ana ci don inganta lafiya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!