Labaran Wasanni
Kocin da ya fara daukarwa kasar Argentina Kofin Duniya, Cesar Luis Menotti ya Rasu
Kocin da ya fara ciyo wa Argentina Kofin Duniya a 1978 César Luis Menotti ya mutu yana da shekara 85, kamar yanda Hukumar Kwallon Kafa ta Argentina ta sanar.
Menotti ya buga kwallo a kungiyoyin Rosario Central da Boca Juniors da kuma Santos.
Ya fara horarwa ne a kungiyar Newell’s Old Boys inda ya lashe gasar zakarun Argentina a 1973, daga nan ne kuma ya zama kocin Argentina a 1974.
Bayan sake samun nasarar lashe Kofin Duniya a 1982, Menotti ya ajiye aiki a matsayin kocin Argentina inda ya koma Barcelona a matsayin koci, inda ya kai kungiyar ga samun nasara a gasar Copa del Rey a shekarar 1983. Ya kuma taba zama kocin Atlético Madrid.
Tuni manyan ‘yan wasa irin su Lionel Messi kyaptin din kasar ta Argentina, da kocin kungiyar kwallon kafa ta kasar mai ci, Lionel Scaloni, suka aike da sakonnin ta’aziyyar mutuwar Menotti.
You must be logged in to post a comment Login