Labarai
Kogin Hadeja Jama’are ba shi da alaka da ambaliyar ruwa a Kano – Ma’um Da’u
Hukumar raya kogunan Hadeja da jama’are ta musanta zargin da wasu kananan hukumomi anan Kano suka yi kan ambaliyar ruwa.
Wannan dai ya biyo bayan yadda wasu kananan hukumomi 8 suka zargi kogin da haddasa musu ambaliyar ruwa a bana.
Shugaban Hukumar Ma’um Da’u Aliyu ne ya bayyana hakan a zantawar sa da Freedom Radiyo.
“Mun yi bincike mun gano cewa kogin Hadeja da Jamare ba shi da alaka da ambaliyar ruwan da aka samu a kananan hukumomin Tarauni, Bunkure Doguwa, Tudun Wada, Minjibir, Rano, Ungoggo da Tsayawa, sai dai mutanen yankunan ne suka zarge shi da haddasa musu, sun manta da yadda ake samun mamakon ruwan sama akai akai. ” in ji Ma’um.
Wannan dai ya biyo bayan wani rahoto da hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kano SEMA ta fitar kan cewa an samu Ambaliya a kanan hukumomi 8 a jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login