Labarai
Gwamna Douye Diri na Bayelsa zai daukaka kara kan soke zaben sa
Gwamnan jihar Bayelsa Douye Diri zai daukaka kara bayan da wata kotun sauraran kararrakin zabe dake zama a babban birnin tarayya Abuja ta a jihar soke zaben sa.
A dai kwanakin baya ne wata tsohon gwamnan jihar Seriake Dickson ya nemi kotun koli ta sake yin nzari kan hukuncin da ta yanke kan zaben gwamnan na jihar ta Bayelsa.
A dai dazu ne wata kotu dake zamanta a birinin tarayya Abuja ta soke zaben Gwamnan jihar Bayelsa Douye Diri, inda ta bada umarnin fara shirye –shirye domin gudanar da wani sobon zabe a jihar.
Mai shari’a Muhammad Sirajo ne ya jagoranci alkalai uku wajen soke zaben, inda ya ce an gudanar da zaben ba bisa ka’ida ba, duba da cewa an cire jam’iyyar PDP da dan takarar ta King George tun a ranar 16 ga watan Nuwanban 2019
Tun da farin dai jam’iyyar hamayya ta PDP ce ta shigar da kara gaban kotu tana kalubalantar hukumar zabe mai zaman Kanta ta kasa kan kin basu dama a ayin zaben.
Tuni dai kotun ta baiwa Hukumar zabe ai zaman kanta ta kasa INEC umarnin sake gudanar da zaben gwamna a jihar a cikin kwanaki 90 masu zuwa.
You must be logged in to post a comment Login