Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotu ta amince a yi Muƙabalar Malam Abduljabbar da Malamai

Published

on

Lauyan nan Barista Ma’aruf Yakasai ya janye buƙatar dakatar da Muƙabala da ya nemi kotu ta yi a kwanakin baya.

A baya dai Barista Yakasai ya nemi, kotun majistiri mai lamba 12 da ke gidan Murtala da ta sanya shi cikin waɗanda ake shari’ar da su, sannan ta dakatar da muƙabalar malamai da Malam Abduljabbar Kabara da Gwamnatin Kano ta shirya.

To sai dai a zaman kotun na ranar Litinin lauya mai kare Ma’aruf Yakasai, Barista Lukman Auwal Abdallah ya janye dukkan ɓuƙatun da suka nema a baya.

Da yake zantawa da Freedom Radio bayan kammala zaman kotun, lauyan ya ce, sun janye buƙatun ne la’akari da sha’awar da mutanen Kano suka nuna na a gudanar da muƙabalar.

A ƙarshe kotun ta amince da janye buƙatun da lauyan ya nema.

Har kawo lokacin da muke haɗa wannan rahoto ɓangaren Gwamnatin Kano bai ce komai ba kan lamarin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!