Labarai
Kotu ta ba da umarni rufe asusun da ake zargin na tsohon gwamnan jihar Lagos
Mai shari’a Chuka Obiozor na babbar kotoun tarayya dake zama a Ikoyin jihar Lagos ya bada umarnin rufe asusun da ake zargin cewa yana da gami da tsohon gwamnan jihar Akinwunmi Ambode wanda yake da fiye da Naira biliyan 9.
A dai ranar 29 ga watan Mayu ne tsohon gwamnan na jihar Lagos Akinwunmi Ambode ya miga ragamar mulkin jihar ga zababan gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu bayan da ya nemi da sake komawa kan kujerar, biyo baya kin goyan bayan jagoran jam’iyyar APC ta kasa Ahamd Bola Tinubu.
Mai shari’a Chuka Obiozor ya yanke hukuncin rufe asusun ne bayan da hukumar EFCC ta shigar da kara kan zargin tsohon gwamnan jihar ta Lagos Ambode na da gami da asusun.
Idai dai hukumar EFCC ta bukaci kotun ta rufe asusun ne har sai an kammala bincike , bayan da aka kama babban sakatare a ofishin shugaban ma’aikata Mr Adewale Adesanua kan zargin.