Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

NNPC zai fara aikin yashe tafkin Chadi da ya Santana ruwa yankin Gongola

Published

on

Kamfanin mai na kasa NNPC ya ce nan gaba kadan ne za’a fara yashe tafkin Chadi da ya dangana zuwa yankin Gongola  ya bi ta Benue bayan da kamfnain ya sami goyan baya daga rundunar sojan kasar nan don kare ma’ikatan sa.

 

Shugaban kamfanin Mele Kyari ne ya bayyana hakan yayin da ya jagoranci manyan hukumomin kamfanin da suka kai zaiyara ga hafsan hafsoshin kasar nan Janaral Gabriel Olonisakin a ofishin sa dake Abuja.

 

Male Kyari ya bukaci al’ummar kasar nan da kada su siyasantar da batun yashe tafkin chadi , yayin da kamfanin ke amfani da dokar ’yancin bada bayanai

 

Shugaban kamfanin mai na kasa NNPC ya kara da cewar sun kai ziyarar ne don neman goyan bayan rundunar sojan kasar nan baya wajen aikin yashe tafkin chadin.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!