Labarai
Kotu ta bukaci Ganduje ya biya Sarki Sunusi diyyar miliyan 10
Wata babbar kotu a birnin tarayya Abuja a ranar Talata, ta nemi gwamnatin jihar Kano da ta nemi afuwa a wajen tsohon sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi na biyu a wasu jaridun Najeriya guda 2.
A hukuncin da kotun ta zartar bisa jagorancin mai shari’a Anwuli Chikere ta ce, tilastawa fitar da sarkin daga jihar bayan cire shi daga muƙamin sa ya saɓa da tsarin mulki da kuma haƙƙin sa na dan adam.
Don haka gwamnatin jihar Kano da ta biya sarkin naira miliyan 10 saboda ɓatanci da aka yi masa.
Idan za a iya tunawa dai, gwamnatin ta sauke sarkin daga muƙamin sa a ranar 9 ga watan Maris na shekarar 2020, bayan an zarge shi da rashin yin biyayya ga gwamnati.
Bayan cire shi ne sarkin ya je kotu domin a binciki halaccin tsare shi da aka yi a ƙauyen loko da ke jihar Nasarawa.
You must be logged in to post a comment Login