Labarai
Kotu ta bukaci hukumar hana fasakwauri biyan diyar naira biliyan 90
Babbar Kotun tarayya da ke Abuja ta zartas da hukuncin hukumar hana-fasakwauri ta kasa ta biya kudin diyya naira biliyan biyar da rabi ga wani kamfani Maggpiy da aka kwacewa shinkafa kwantena 90 ba bisa ka’ida ba.
Hukuncin Kotun na jiya laraba ya zo ne bayan da kamfanin ya shigar da karar cewa jami’an Custom sun yi dirar mikiya a wajen ajiye kayayyaki na kamfanin da ke garin Kalaba ranar 18 ga watan Maris din shekarar 2017 tare garkame wurin.
Kamafanin ya shaidawa Kotun cewa baya ga garkame wajen ajiyarsu da hukumar ta yi, ta kuma kame wasu kwantenoni 317 na shinkafa a garin Fatakwal na tsawon watanni 4 ba bisa ka’ida.
Da ya ke yanke hukuncin Justice Inyang Ekwo, amince da korafin kamfanin inda ya ce hukumar ta Customs tare da shugabanta sun sabwa doka.
Justice Ekwo ya nuna bacin ransa kan yadda wasu jami’an Customs suka rinka sace shinkafar a cikin kamfanin da aka garkame.
Haka zalika alkalin ya wanke mashawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro daga zargin hannu cikin kama shinkafar