Labarai
Kotu ta dage sauraron shari’ar malam Ibrahim Shekarau
Wata Kotun tarayya mai zamanta a nan Kano ta dage sauraron Shari’ar da ta ke yi wa tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau da tsohon Ministan harkokin waje Aminu Wali da kuma wani tsohon Kwamishina a nan Kano Mansur Ahmad.
Mai Shari’a Zainab Abubakar Bage ce ta sanar da hakan a safiyar yau, inda ta tsayar da ranar 18 ga watan Oktoba mai zuwa domin ci gaba da sauraron Shari’ar.
A safiyar yau ne dai mutane ukun suka halarci zaman kotun kan zargin da hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa ta yi musu, kan badakalar kudi Naira miliyan 950 da take zargin sun karba na yakin neman zaben shekarar 2015.
Lauyan EFCC Jonhson Ojogbemi, ya bukaci kotun ta mayar da Shari’ar zuwa birnin tarayya Abuja bisa dalilan tsaro, sai dai Lauyan Malam Ibrahim Shekarau Sam Ologunorisa, ya nuna rashin amincewarsa da wannan bukata kasancewar hakan ya saba da tsarin bad belin wadanda ake zargi, kuma wata barzanar tsaro da ake fuskanta.
Wakilinmu Bashir Muhd Inuwa ya rawaito cewa a yanzu haka dai sai ranar 18 ga watan Oktobar ne sannan kotun za ta yanke hukunci kan wannan Shari’a ko za a mayar da Shari’ar Abuja ko akasin haka.