Labarai
An saka ranar da za a buga wasan El Classico

Hukumar kwallon kafa ta kasar Spain ta saka ranar da za a fafata wasan hamayya na El Classioc tsakanin Barcelona da Real Madrid zagaye na biyu.
Wasan zai gudana ne a ranar 11 ga watan Mayu, a wasan mako na 35 a filin wasa na Estadi Olimpic Lluis Companys.
Barcelona ce ke jagorantar teburin gasar da tazarar maki hudu tsakanin ta da Real Madrid dake mataki na biyu.
You must be logged in to post a comment Login