Manyan Labarai
Kotu ta dakatar da gwamnatin Kano daga aiwatar da sabuwar majalisar sarakuna
Babbar kotun jihar Kano karkashin jagorancin mai shari’a A.T Badamasi ta dakatar da gwamantin jihar Kano daga karkirar majalisar sarakunan Kano.
Majalisar dai wadda aka tsara zata kunshi Sarkin Kano Malam Muhammad Sunusi na biyu da Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero da na Rano Tafida Abubakar Ila sai Sarkin Karaye Alhaji Ibrahim Abubakar da Sarkin Gaya Ibrahim Abdulkadir.
A ranar talatar da ta gabata ne gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta ayyana mai martaba sarkin Kano Malam Muhammad Sunusi na biyu a matsayin shugaban majalisar ta sarakunan jihar Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa masu zabar sarki a masarautar Kano wanda suka hada da Madakin Kano Yusuf Nabahani da Makaman Kano Abdullahi Sarki Ibrahim da sarkin Dawaki mai tuta Bello Abubakar da kuma Sarkin Bai Mukhtar Adnan ne sune suka shigar da karar suna kalubalantar kafa majalisar ta sarakunan jihar Kano.