Kiwon Lafiya
Kotu ta dakatar tsige mataimakin gwamnan jihar Imo
Mai shari’a Ben Iheka ya bayyana hakan ne a yau Litinin cikin wani umar ni da ya bayar.
Rahotanni sun ce babban jojin jihar ta Imo ne ya kafa kwamitin domin gudanar da bincike kan zargin da majalisar dokokin jihar kewa mataimakin gwamnan na rashin da’a.
Mai shari’a Iheka ya kuma bada umarci mambobi uku na kwamitin su dasu girmama wannan umarni na kotu da ya dakatar da yunkurin tsige mataimakin gwamnan.
Lauyan mataimakin gwamnan Ken Njemanze ya shedawa kotun cewar a shirye suke su bawa kotun hadin kai ta gudanar da shari’a kan wannan yunkuri na tsige shi daga mukamin sa.
Ya ce sun dogara da kotun cewar zata yi adalci domin kare mutuncin lamba biyun na jihar Imo da kuma martabar ofishin mataimakin gwamna.
Bayan sauraron lauyan ne kuma mai shari’a Ben Iheka ya amince da bukatar mai kara, sannan ya dage zaman zuwa 13 ga watan gobe.