Labarai
Kotu ta kawo ƙarshen takaddamar iyakokin ƙasa da ke tsakanin Najeriya da Kamaru – Malami
Gwamnatin tarayya ta tabbatar da kawo karshen taƙaddamar iyakokin ƙasa da ke tsakanin Najeriya da Kamaru.
Attoni Janar kuma ministan shari’a Abubakar Malami ne ya bayyana hakan a wata ziyara da ya kai wa Jakadan majalisar dinkin duniya mai kula da Yammacin Afirka Mahamat Annadif.
Malami ya tabbatar da cewar kotun duniya ta kammala yanke hukunci tsakanin ƙasashen biyu, ta hanyar fitar da iyakokin ƙasashen biyu kowacce akwai iya inda ta mallaka.
A nasa jawabin jakadan na majalisar ɗinkin duniya Annadif ya ce, majalisar za ta ci gaba da haɗa kan mambobin ƙasashen wajen ganin an samu kyakyawar alakar diflomasiyya da zaman lafiya.
You must be logged in to post a comment Login