Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Halin da yaran Kano waɗanda aka gano a Anambra ke ciki bayan shekara guda

Published

on

Sama da shekara guda kenan da ceto wasu ƙananan yara 9 da aka sace daga nan Kano zuwa jihar Anambra.

Galibi dai yaran sun samu sauye-sauye wajen gudanar da rayuwarsu.

Waɗanda suka haɗa da sauyin yare, addini dama al’ada.

Yadda rayuwar yaran ta ke a yanzu
Freedom Radio ta ziyarci wasu cikin yaran domin ganin halin da suke ciki.

Jamila Ado Sani ita ce mahaifiyar Faruk Ibrahim wanda ya shafe shekaru biyar a can.

Ta ce, yanzu an ɗan samu sauyi, domin yanzu yana ci gaba da gudanar da al’amuransa na addini.

Haka ma yana zuwa makarantar islamiyya sai dai abokan karatunsa sun bashi tazara.

Amma ana wareshi a wasu lokutan domin yi masa muraja’ar darusan baya.

Jamila Ado Sani mahaifiyar Faruk

Dangane da abinci mahaifiyarsa ta ce har yanzu bai gama sabawa da abincin da ake yi a nan ba.

Ta ce, farkon dawowarsa da cokula biyu ya ke cin abinci.

Ɓangaren sanya sutura ma mahaifiyarsa ta ce, an samu ci gaba.

“Yanzu yana sha’awar sanya kayan malam bahaushe maimakon ɗaura zani da yake yi a baya” a cewarta.

Ta ƙara da cewa, babban abin da ke damunsu a yanzu, shi ne yawan firgita da yaron ke yi.

A wasu lokutan kuma ya riƙa surutan cewa ana biyo shi.

Shi kuwa Umar Faruk ɗin ya shaidawa Freedom Radio cewa har yanzu yana tuno abubuwan da suka faru da shi a Anambra.

Sai dai babban abin da ke ci masa tuwo a ƙwarya shi ne yadda ake nuna masa ƙyama a makaranta.

Ya ce, “malamarmu ma na kyara ta saboda rashin iya Hausa, tana cewa ni ba ɗan Kano ba ne”.

Malam Ibrahim Ahmad Salisu mahaifin Faruk

Malam Ibrahim Ahmad Salisu shi ne mahaifin Faruk ya ce, suna iya bakin kokarinsu wajen ganin an magance sauye-sauyen da yaron ya samu.

Ɓangaren sauran yaran
Sauran yaran ma dai sun fara samun ci gaba kan sauye-sauyen da suka samu.

Malam Muhammad Abdullahi shi ne mahaifin Aisha da ta yi shekara 4 a Kurmi bayan sace ta, wadda aka sauya mata suna zuwa Ozioma.

Malam Muhammad Abdullahi mahaifin Aisha

Ya ce, yanzu haka rayuwarta ta fara daidaita a ɓangaren addini da kuma abinci.

Freedom Radio ta iske Aisha tana tsaka da karatun alƙur’ani mai girma.

Malam Salisu Isah shi ne mahaifin Husna Isah wadda ita ba ta ɗauki tsawon lokaci a Anambran ba aka gano su.

Malam Salisu Isah mahaifin Husna

Ya ce, sannu a hankali tana dawowa cikin dabi’ar Malam Bahaushe.

Meye matsayar iyayen kan shari’a?
Iyayen yaran sun ce ba a tuntuɓar su game da yadda shari’ar ke gudana, sai dai kawai suna jin labari a Radio.

Karanta karin labarai:

Kano 9 Kids: Yara 113 aka sace daga Kano zuwa Kudu – Kwamitin bincike

Kano9: Abubuwan da suka faru kan yaran Kano da aka sace cikin shekara guda

Bonono wai rufe ƙofa da ɓarawo
Wata majiya ta tabbatar mana da cewa yara 9 da aka gano a wancan lokaci 7 daga ciki ne ƴan asalin jihar Kano.

Kuma su ne aka miƙa su ga iyayensu haɗe da tukuicin naira miliyan guda-guda da gwamna ya basu.

Sauran yara biyu kuma an mayar dasu jihar Anambra haɗe da wancan tukuici na miliyan guda-guda saboda rashin gano iyayensu.

To ko ina matsayar rundunar ƴan sandan Kano da kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa?

Zamu ci gaba da bibiya a nan gaba.

Ku kalli wannan rahoto cikin bidiyo

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!