Labarai
Kotu ta sallami matar da ake zargi da satar yara 3 a Kano
Kotun ɗaukaka ƙara ta sallami matar nan mai suna Love ogar wadda ake tuhuma da satar yara 3 a Kano.
Kotun karkashin mai shari’a Ita I. George Mbaba ita ce ta warware hukuncin kotun jiha karkashin mai shari’a Aisha Mahmud.
Tun a shekarar 2014 aka kama Love Orgar a Kaduna Inda ake tuhumarta da sato yara uku da suka haɗar da Khalid Muhammad da Abdul Muhammad da kuma Nafiu Muhammad a unguwar Badawa.
A shekarar 2019 kotun ta yanke mata hukuncin zaman gidan gyaran hali na shekaru 9 da biyan kuɗi Naira dubu dari biyu da aiki mai tsanani.
Hakan yasa Lauyan ta Ya’u Abdullahi ya garzaya kotun ɗaukaka ƙara domin rashin gamsuwar sa da hukuncin.
A zaman kotun na ranar Laraba 27 ga watan Oktobar 2021 mai shari’a Ita Mbaba ya yi karatun baya inda ya rusa hukuncin farko.
Bayan fitowa daga kotu Freedom Radio ta zanta da lauyan gwamnati Barista Lamido Soran Ɗinki wanda shi ne mai gabatar da ƙara ya kuma ce za su tafi kotun Ƙoli.
Shima lauyan wadda aka sallama Barista Ya’u Abdullahi ya bayyana farin cikinsu da hukuncin da kotu ta yi.
You must be logged in to post a comment Login