Labarai
Kotu ta umarci ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa su janye yajin aiki da su ke yi cikin gaggawa
Kotun ɗa’ar ma’aikata ta ƙasa da ke zaman ta a Abuja ta umarci ƙungiyar Likitoci masu neman kwarewa NARD, da ta janye yajin aikin da ta fara tun ranar 2 ga watan Agusta.
A zaman kotun na yau Juma’a mai shari’a Bashir Alkali ya umarci ƙungiyar NARD ta dakatar da yajin aikin da ta ke yi cikin gaggawa, bayan da ya saurari dukkanin ɓangarorin da lamarin ya shafa.
Umurnin ya biyo bayan ƙarar da gwamnatin tarayya ta shigar gaban kotun domin ƙalubalantar halaccin yajin aikin na su.
Tuni dai gwamnatin tarayya da ma’aikatar lafiya ta ƙasa suka dage kan cewa, kungiyar NARD ta fara yajin aikin a daidai lokacin da bai dace ba, kuma ba su yi shi akan ƙa’ida ba.
You must be logged in to post a comment Login