Labarai
Kotu ta yanke wa matashin da ya ƙona masallata hukuncin rataya

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kano, a ranar Litinin, ta yanke wa wani mutum mai suna Shafi’u Abubakar, mai shekaru 38 hukuncin kisa ta hanyar rataya da kuma yi masa bulala 150 bisa laifin cinna wa wani masallaci wuta tare da kashe mutane 23.
Abubakar, wanda ke zaune a karamar hukumar Gezawa, a Kano ana tuhumarsa da laifin kisan kai haddasa munanan raunuka da kuma barna ta hanyar tada wuta.
Da yake yanke hukuncin, alkalin kotun Malam Halhalatu Khuza’i-Zakariyya, ya ce daga cikin shaidu bakwai da masu gabatar da kara suka gabatar, shaidu biyu ne kawai suka tabbatar da lamarin ba tare da wata shakka ba.
Ya ce shaida na 1 da na 2 sai na 3 da na 5 da kuma 6 duk labari kawai suka bayar yayin da ya kawo wani rubutu na addinin Musulunci, da ya ce ba su nan a lokacin da lamarin ya faru ba, labari kawai suka ji, wasu kuma sai suka ga wuta a masallaci.
Alkalin kotun ya yanke wa wanda ake tuhuma hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsa da laifin kisan kai da kuma yi masa bulala 100 bisa laifin yunkurin kisan kai.
Ya kuma umurci wanda ake kara da ya biya tarar Naira 1,500 saboda ya yi mugun rauni da kuma bulala 50 na tayar da wuta.
Khuza’i-Zakariyya ya kuma umurci gwamnatin jihar da ta karbi babur uku na wanda ake kara a sayar da su domin gyara masallacin da aka kona.
Alkalin ya kuma bayyana cewa, wanda aka yanke wa hukuncin ya na da kwanaki 30 don daukaka kara a hukuncin.
Lauya mai gabatar da kara ya ce, matashin ya aikata laifin ne a kauyen Gadan da ke Larabar Abasawa a karamar Hukumar Gezawa ranar 15 ga Mayu, 2024.
You must be logged in to post a comment Login