Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Kotu ta yankewa shugaban kungiyar direbobin hanya ta kasa reshen jihar Lagos hukuncin kisa

Published

on

Wata babbar kotun tarayya dake zama a Ikeja dake jihar Lagos, ta yanke hukuncin kisa ga Saheed Arogundade, shugaban kungiyar direbobin hanya ta kasa reshen jihar Lagos, saboda kashe wani dan sanda Gbenga Oladipupo mai shekaru 32.

Kamfanin dilancin labaru na kasa NAN ya rawaito cewa mai shari’a Olabisi Akinlade ta kama Arogundade da laifin kisa tare da wasu mutum 5 da suka hada Mustapha Layeni da Adebayo Abdullahi da Seyi Pabiekun da Sikiru Rufai da Yusuf Arogundade.

A yayin yanke hukuncen da ya kwashe awa 3 ana  yi da aka kafara da misalin karfe 2 da rabi, mai shair’a Olabisi ta ce wanda ake zargi ya gaza bada hojojin da kotu zata gamasu bas hi ya aikata kisan ba.

Haka zalika Kafin yanke hukuncin, mai shari’ar saboda dalilan tsaro ta nemi a kule akwatin da ake zargin mai laifi na tsaya wa a ciki, a kuma ajiye mukin cikin wani akwati bayan kammala hakan ne, ta bayyana cewar kotun ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda laifin d aya aikata.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!