Connect with us

Labarai

Kotu ta yanke wa mutane biyu hukuncin kisa bisa yin garkuwa da jami’in NYSC

Published

on

Babbar Kotun Jihar Ekiti ta yanke wa wasu mutane biyu, Ibrahim Abubakar da Abdullahi Abubakar, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta same su da laifin yin garkuwa da wani jami’in Hukumar NYSC, Omoboade Adesina.

 

Kotun ta ce, an tabbatar da laifinsu ba tare da wata shakka ba, yayin da ta wanke mutum na uku, Usman Abubakar, saboda rashin isassun hujjojin da suka danganta shi da laifin.

 

Yayin da yake yanke hukunci, Alkalin Alkalan Jihar Ekiti, Mai Shari’a Lekan Ogunmoye, ya bayyana cewa shaidar tantance wadanda ake zargi da kuma bayanan kiran waya da aka tantance, sun taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da cewa Ibrahim da Abdullahi ne suka aikata laifin. 

 

Saboda haka kotun ta yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya, yayin da ta sallami tare da wanke Usman Abubakar daga dukkan tuhume-tuhumen da ake masa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!