Labarai
Kotu ta yankewa wasu tsoffin ma’aikatan banki hukuncin dauri a Kano
Babbar Kotun Jihar Kano karkashin jagorancin Mai Shari’a Farouq Lawan a ranar Laraba ta aike da Jude Ameh da Ademola Aderibigbe gidan gyaran hali bisa zargin sata.
Ana dai zargin mutanen biyu da hada baki tare da damfarar wanda ya shigar da kara kotu kudi naira Miliyan goma sha daya da dubu dari uku da sittin (11,360,000) don amfanin kansu.
Bayan da aka gurfanar da ma wadanda ake zargi, sun ce ba su da laifi a kan tuhume-tuhume 17 da aka gabatar musu.
Lauyan mai shigar da kara Salihu Sani ya bukaci ranar da za a ci gaba da shari’a.
A ci gaba da sauraron batun, wadanda ake zargin sun amince da aikata laifin da ake tuhumarsu kuma sun nemi da a saukaka musu hukuncin.
Ganin sabon rokon nasu, lauyan masu shigar da kara, Sani ya roki kotu da ta yanke masu hukunci daidai da laifin.
Bayan haka, Mai Shari’a Lawan ya yanke musu hukuncin daurin shekaru biyu a gidan gyaran hali tare da zabin tarar naira Dubu Dari (N100, 000).
You must be logged in to post a comment Login