Kiwon Lafiya
Kotun daukaka kara da ke ta yi watsi da bukatar Onnoghen na hana kotun da’ar ma’aikata ci gaba da tuhumarsa
Kotun daukaka kara da ke zaman ta a Abuja ta yi watsi da bukatar dakataccen babban jojin Najeriya Mai shari’a Walter Samuel Onnoghen na cewa ta hana kotun da’ar ma’aikata ci gaba da sauraren tuhumar da ake yi masa.
Kotun mai alkalai 3 karkashin jagorancin mai shari’a Abdul Aboki a wani hukunci da ta yanke a yau Laraba ta yi watsi da bukatar tasa, inda ta ce babu yadda za’a yi ta yi katsalandan a cikin shari’ar da aka riga aka fara musamman ta babban laifi.
Kotun ta kuma kara da cewa idan aka yi la’akari da sashen na 306 na dokar manyan laifuka, kotun ta ce bata da hurumin dakatar da manyan laifuka da ake kira Criminal Cases a turance.
Bisa wannan hukunci da kotun ta yanke a yanzu haka kotun da’ar ma’aikata tana da damar ci gaba da tuhumar shi Onnoghen, idan kuma ta kammala ta yanke hukunci a kai.