Kiwon Lafiya
Kotun daukaka kara ta soke karar da Onnoghen ya shigar gabanta
Kotun daukaka kara dake Abuja ta soke daukaka karar da dakataccen babban jujin kasar nan Walter Onnoghen ya shigar gaban ta.
Kotun ta ce karar an rigaya an saurare ta a kotun da’ar ma’aikata kuma tuni ma da aka kammala sauraran ta a kotun.
A yayin da ake yin shari’ar karkashin jagorancin mai shari’a Stephen Adah, kotun daukaka kara ta ce umarnin gaggawa da kotun da’ar ma’aikata ta bayar ya saba wa damar da dakataccen babban jujin kasar nan yake da shi nayi masa adalci yayin sauraran da yanke hukuncin karar.
Kotun daukaka karar ta bayyana cewa babu bukatar dakataccen babban jojin Najeriya ya kalubalanci umarnin gaggawar da kotun da’ar ma’aikata ta bayar na cewa babban jujin kasar nan Walter Onnoghen ya sauka daga kan mukamin sa.
Dalilin haka ne kotun ta yi watsi da daukaka karar da babban jujin ya yi sakamakon umarnin da shugaban kotun da’ar ma’aikata, mai shara’a Danladi Umar ya baiwa Walter Onnoghen da ya sauka daga kan mukamin sa na babban jujin kasa har sai an kammala shari’ar da ake masa na kin bayyana wasu daga cikin kadarorin da ya mallaka