Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Rundunar ‘yan sandan jihar katsina ta kama mata hudu dake taimakawa ‘yan ta’adda

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce ta kama wasu mata guda hudu wadanda suke karnukan farautar ‘yan bindiga ne a jihar.

A cewar rundunar, ‘yan bindigar samaruka ne ga matan wadanda suke dafa musu abinci da sauran biya musu wasu bukatun su.

Mai Magana da yawun rundunar SP Gambo Usah ya ce an kama matan ne yayin wani samame da aka kai musu.

Matan sune Bilkisu Abubakar mai shekara ashirin da Rasikat Amadi da Sulie Dairu masu shekara arba’in da biyar da kuma Rakiyar Yusuf mai shekru ashirin.

Mai magana da yawun ‘yan sandan ya kuma ce matan suna yawan ziyartar dajin Rugu domin kaiwan rahotannin abubuwan da ke faruwa a gari ga ‘yan bindigar.

Haka zalika an kuma gano cewa mafi yawa na ‘yan ta’addar da ake nema ruwa a jallo suna alaka da matar ciki kuwa har da Roga Kachalla da Gume Basullube da Sumail da Haruna Dum da Auta Kachalla da Yauza Mai-Bakarkama da Lawali Adda da kuma Babanyara da kuma Dogo.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!