Labarai
Kotun koli a Nijeriya ta umarci CBN daya dage ranar daya tsayar don daina amfani da tsaffin kudade a kasar
Kotun kolin a Nijeriya da ke zamanta a Abuja ta ba da umarnin dakatar da gwamnatin tarayya daga daina amfani da tsoffin takardun kudi da ta tsara farawa daga 10 ga watan Fabrairun nan da muke ciki.
Tawagar alkalan kotun, karkashin jagorancin John Okoro, ta shaidawa kotun cewa sun shigar da karar ne biyo bayan korafe–korafen da gwamnonin jihohin Arewacin kasar nan da suka hadar da Kaduna da Kogi da kuma Zamfara suka yi kan matakin.
Da yake mika bukatar ga alkalin kotun lauyan masu kara A.I.Mustapha SAN, ya jaddada bukatar janye dokar, la’akari da halin matsi da al’ummar Najeriya suka shiga na kuncin rayuwa, inda ma wasu bankuna suka fara rufewa.
Kotun ta ba da umarnin ne na wucin gadi ga babban bankin kasa CBN da ya dakatar da daina amfani da kudin.
Rahoton: Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa
You must be logged in to post a comment Login