Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotun koli a Nijeriya ta umarci CBN daya dage ranar daya tsayar don daina amfani da tsaffin kudade a kasar

Published

on

Kotun kolin a Nijeriya da ke zamanta a Abuja ta ba da umarnin dakatar da gwamnatin tarayya daga daina amfani da tsoffin takardun kudi da ta tsara farawa daga 10 ga watan Fabrairun nan da muke ciki.

Tawagar alkalan kotun, karkashin jagorancin  John Okoro, ta shaidawa kotun cewa sun shigar da karar ne biyo bayan korafe–korafen da gwamnonin jihohin Arewacin kasar nan da suka hadar da Kaduna da Kogi da kuma Zamfara suka yi kan matakin.

Da yake mika bukatar ga alkalin kotun lauyan masu kara A.I.Mustapha SAN, ya jaddada bukatar janye dokar, la’akari da halin matsi da al’ummar Najeriya suka shiga na kuncin rayuwa, inda ma wasu bankuna suka fara rufewa.

Kotun ta ba da umarnin ne na wucin gadi ga babban bankin kasa CBN da ya dakatar da daina amfani da kudin.

Rahoton: Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!