Labaran Kano
Kowa yazo ya dauki dan sa daga makarantun Mari ko mu dauki mataki –Gwamnatin Kano
Shugaban kwamitin tsaftace makarantun Mari da gyaran tarbiya, Dr Muhammad Tahar Adamu Baba impossible ya bayyana cewar an dauki matakin rufe makarantun Yan Mari ne, saboda kaucewa fatattakarsu ta karfin tuwo kamar yadda akayi a wasu jihohin.
Dr Baba impossible wanda shine kwamishinan harkokin addini na Kano yace ya zama wajibi ga dukkan makarantun su mayar da daliban ga iyayen su, idan kuma iyayen basu karbi yayan ba to kowanne Malami ya Mika daliban dake hannun sa ga hukumar Hisbah kafin karewar wa’adin lokacin da aka bayar.
Dr. Muhammadd Tahar Adamu ya bayyana cewar gwamnati zata fito da hanyoyin samar da mafita ga wadanda aka saka amma wajibi ne akan kowanne uba ya dauki alhakin tarbiyyar yayansa.
Rubutu masu nasaba:
Menene makomar ‘Yan Mari bayan da gwamnati ta soke ayyukan su.
Gwamnatin Kano ta soke Makarantun ‘Yan Mari
‘Yan mari 36 sun shaki iskar ‘yanci a Kano