Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kaduna

Kowanne mai motar haya ya tabbatar yayi fenti ruwan ɗorawa – El-rufai

Published

on

Gwamnatin jihar Kaduna ta umarci masu motocin haya da su tabbatar sun yiwa motocin su fenti kafin wa’adin da aka ba su.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a zantawar sa da manema labarai.

Aruwan ya ce, wa’adin da gwamnati ta bai wa masu motocin haya na yin fenti ruwan ɗorawa zai cika ne nan da kwana 30.

Kwaminshinan tsaro Samual Aruwan ya ce, wannan mataki ne na magance matsalolin tsaron da ake fuskanta a jihar.

Ya jaddada cewa “gwamnatin ta hana sayar da mai na bunburutu a wasu daga cikin ƙananan hukumomi jihar irinsu Kaciya, Birnin Gwari Igabi Chikun da kuma Kajuru”.

Tuni dai gwamnatin jihar ta ayyana cewa za ta katse hanyoyin sadarwa a wasu ƙananan hukumomi da suka fi fuskantar matsalar tsaro.

Haka kuma a gobe ne dai dokar hana hawan babubura na tsawon wata uku zai fara aiki.

cikin jihar da Hana yin anfani da duk wani makami indai ba jamian tsaro ba suma masu baburan adai daita daita su ayikinsu

nasa 6

zuwa 7 na yamma da Kuma haramta musu saka labule ajikin adaidaita sahun .

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!