Labarai
Ku guji amfani da jihohin Kano da Jigawa wajen fasakwaurin kayayyaki – Kwastam
Hukumar yaki da fasawauri ta kasa kwastam ta gargadi masu fasakwaurin kayayyaki da su guji amfani da shiyyar Kano wajen aikata miyagun ayyukansu domin kuwa hukumar a shirye ta ke da ta ladaftar da duk wanda ta kama yana safarar kayayyaki ba isa ka’ida ba.
Kwanturolan hukumar mai kula da shiyyar jihohin Kano da Jigawa Sulaiman Umar ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai yau anan Kano.
Ya ce, tsakanin watan Janairu zuwa Maris hukumar ta kama kayayyaki da aka shigo da su ba bisa ka’ida ba, da suka hada da: shinkafa ‘yar waje, taliya, Macaroni da kayan gwanjo da madara da sabulai da kuma tsofaffin tayoyi.
A bangare guda hukumar ta kwastam shiyyar jihohin Kano da Jigawa ta kuma tara haraji da ya kai naira biliyan bakwai da miliyan dari shida da hamsin da takwas da dubu dari da talatin da takwas da dari shida da hamsin da tara, cikin wa’adin watanni uku.
A cewar hukumar wannan adadi ya zarce na watanni ukun farko a shekrara da ta gabata wanda hukumar ta tattara naira biliyan uku da miliyan dari takwas da casa’in da takwas da dubu dari shida da bakwai da naira talatin da bakwai kacal.
You must be logged in to post a comment Login