Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ku karanta jawabin da shugaba Buhari yayi kan kasafin kuɗin 2022

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kuɗin baɗi na naira tiriliyan 16 da biliyan 39 ga majalisun tarayyar ƙasar nan, don neman sahalewarsu a kai.

Shugaban majalisar dattijai Sanata Ahmad Lawan ya sha alwashin cewa za su sahalewa kasafin kafin karewar shekarar nan da muke ciki.

Da yake gabatar da jawabi ga haɗakar zauren majalisun tarayyar ƙasar nan, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi wa kasafin take da “kasafin bunƙasa tattalin arziƙi domin ɗorewar haɓakar tattalin arziƙin”.

Ya ce kasafin zai mayar da hankali ne wajen faɗaɗa komar tattalin arziƙin, tare da karfafa ƙanana da matsakaitan masana’antu da kyautata harkokin tsaro da tabbatar da shugabaci nagari, sai bunƙasa fannonin ilimi da kiwon lafiya da kuma takaita fatara, da dai sauransu.

”ya ce ɓangaren zartarwa zai haɗa kai da majalisun tarayya domin tabbatar da cimmawa da kuma sahalewar kasafin na baɗi, kafin ƙarewar shekarar 2021, ta yadda kasafin zai fara aiki daga watan Janairun baɗi.

Shugaba Buhari “Ya kuma ce kasafin kuɗin baɗi, shi ne na ƙarshe da gwamnatina za ta bibiya har zuwa ƙarshensa”.

Ya ce “Gwamnatinsa ta tsara kasafin ne domin ɗorawa a kan ayyukan da ta faro a cikin kasafin bana na gina ƙasa har zuwa shekarar 2025”.

“Masu girma ‘yan majalisa, ina fatan za ku nazarci kasafin tare da yin la’akari da halin da duniya take ciki, gami da ci gaban da muka cimma, a daidai lokacin da duniyar ke farfadowa daga annobar cutar Covid-19 da ta addabi duniya, kuma muna ci gaba da bin dukkan ka’idojin yaki da cutar, don kare al’umma”.

Shugaba Buhari ya ce babban abinda gwamnatinsa za ta ci gaba da mayar da hankali a kai shi ne tsaro da kuma kammala ayyukan da ya faro.

Kasafin ƙudin na 2022, wanda ya kai naira tirliyan 16 da ɗigo 39, ƙari ne a kan naira tiriliyan 13.98 na kasafin ƙuɗin shekara 2021.

Shugaban ƙasar ya bayyana shrin gwamnatinsa na ciyo bashi don samun ƙarin ƙudi har Naira tiliyan 6 da biliyan 258, da za ta cike giɓin da za a samu a kasafin kuɗin da shugaban zai gabatar na shekarar 2022.

Daga cikin kuɗin da shugaban ƙasar ya gabatar a kasafin kuɗin na 2022, har da muhimman ɓangarorin da za a warewa kuɗaɗe kamar hukumar zaɓen INEC, wadda ake sa ran tanadar mata ƙarin naira biliyan 100, don shirin tunkarar babban zaben 2023.

A yayin gabatar da kasafin kuɗin dai, shugaba Buhari ya sanar da ajiye gangar man fetir ɗaya a kan farashin dala 57, da kuma haƙo man fetir ganga kusan miliyan biyu a kullum.

Sai kuma canjin dala daya a kan Naira 410 da silai 15, da kuma hasashen samun kuɗin shiga Naira tiriliyan 3 da ɗigo 15 daga ɓangaren man fetur.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!