Labarai
Kudaden da ake gebewa makarantun kimiyya da fasaha sun yi karanci – Majalisa
Majalisar wakilai ta koka kan karancin kasafin kudaden da gwamnatin tarayya ke warewa ma’aikatar kimiyya da fasaha don gudanar da ayyukan su.
Shugabar kwamitin majalisar kan ma’aikatar kimiyya da fasaha ta kasa Beni Lar daga jihar Plateau ce ta bayyana haka ga manema labarai a birnin tarayya Abuja a lokacin ziyarar aiki a ma’aikatar a farkon makon nan.
Beni Lar ta ce abin takaici ne kwarai ace Gwamnatin tarayya na ware kaso kasa da digo biyu a cikin kasafin kudin Gwamnatin tarayya.
Beni Lar ta ce duk da dumbin ma’aikatun da hukumar ke dasu da zasu kawo wa kasar nan ci gaba da dimbin kudaden shiga, kama da ga harkokin noma zuwa tsaro da sana’o’i abin takaici ne da gwamnatin tarayya tayi halin ko in kula da su.
Ta kara da cewa lokaci yayi da Gwamnatin tarayya zata yi amfani da hukumar don samo sabbin kirkire-kirkire da fasahar zamani da za su samar wa da kasar nan kudaden shiga.
You must be logged in to post a comment Login