Labaran Kano
Kudin da ‘yan fansho ke amsa ya yi kankata- Hamza Sule Wuro-Koki
Shugaban hukumar kula da Asusun Fanshon ‘yan sanda Hamza Sule Wuro-Koki ya ce jami’an ‘yan sanda da suke shirin yin retaya a wannan shekarar su mai da hankali wajen yin amfani da wannan damar wajen yin abubuwa masu muhimmanci da zai inganta rayuwarsu.
Shugaban ya bayyana haka ne a yayin da ake taron karawa juna sani da aka shirya wa jami’an ‘yan sanda da suke shirin ritaya a wannan shekarar.
Ya kara da cewa duk da kokarin da hukumar take yi don inganta rayuwar ‘yan sandan, babban kalubalen da suke fuskata shine rashin isashin kudin fansho da suke karba bayan kammla aiki.
Gwamnatin jihar Kano ta musanta zargin sauya wa ‘yan fansho tsarin karbar fansho
‘Yan Fansho na jiran kudaden su a Kano
Gwamnatin Jigawa ta biya fiye da naira biliyan 5 hakokin ‘yan fansho
A nasa bangaren shugaban sasshen kula da hakkin masu ritaya na ‘yan sanda Mustapha Suleman ya bayyana cewa wannan shine karo na hudu da hukumar ta shirya irin wannan taron kuma zasu cigaba da gudanar da taron kasancewar yana da muhimmamnci.
Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa taron ya samu halartar manyan jami’an ‘yan sanda da wasu daga cikin ma’aikatan hukumar fansho na yan sanda da dai sauransu.