Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Kudin da ‘yan fansho ke amsa ya yi kankata- Hamza Sule Wuro-Koki

Published

on

Shugaban hukumar kula da Asusun Fanshon ‘yan sanda Hamza Sule Wuro-Koki ya ce jami’an ‘yan sanda da suke shirin yin retaya a wannan shekarar su mai da hankali wajen yin amfani da wannan damar wajen yin abubuwa masu muhimmanci da zai inganta rayuwarsu.

Shugaban ya bayyana haka ne a yayin da ake taron karawa juna sani da aka shirya wa jami’an ‘yan sanda da suke shirin ritaya a wannan shekarar.

Ya kara da cewa duk da kokarin da hukumar take yi don inganta rayuwar ‘yan sandan, babban kalubalen da suke fuskata shine  rashin isashin kudin fansho da suke karba bayan kammla aiki.

Gwamnatin jihar Kano ta musanta zargin sauya wa ‘yan fansho tsarin karbar fansho

‘Yan Fansho na jiran kudaden su a Kano

Gwamnatin Jigawa ta biya fiye da naira biliyan 5 hakokin ‘yan fansho

A nasa bangaren shugaban sasshen kula da hakkin masu ritaya na ‘yan sanda Mustapha Suleman ya bayyana cewa wannan shine karo na hudu da hukumar ta shirya irin wannan taron kuma zasu cigaba da gudanar da taron kasancewar yana da muhimmamnci.

Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa taron ya samu halartar manyan jami’an ‘yan sanda da wasu daga cikin ma’aikatan hukumar fansho na yan sanda da dai sauransu.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!