Connect with us

KannyWood

Kun san jaruman da sukafi yawan mabiya a Kannywood?

Published

on

Dandalin sada zumunta na Instagram shi ne shafin da jarumai da kuma masu hurda da masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood sukafi maida hankali akan sa.

Babu shakka ga duk wanda ke neman wata gulma ko tsokaci game da masana’antar Kannywood to kawai yayi amfani da shafin Instagram domin ganin dukkan wainar da ake toyawa a masana’antar.

A yayinda shekara ta 2019 ke bankwana Freedom Radio ta bibiyi manyan jaruman dake amfani da dandalin na Instagram inda muka zakulo muku mutane goma sha daya da suke da yawan mabiya a masana’antar.

Jaruma Rahma Saudau

Rahma Sadau: Ita ce wadda tafi kowane jarumi a masana’antar Kannywood yawan mabiya a dandalin Instagram inda take da mabiya har kimanin miliyan daya da dubu dari bakwai, ba iya nan Rahma Sadau ta tsaya ba, domin kuwa ita ce ta kere dukkan al’ummar Hausawa yawan mabiya a dandalin na Instagram.

Rahma Sadau tana cikin jaruman da akafi cece kuce akansu a kafafan sada zumunta a wannan shekara da muke bankwana da ita ta 2019.

Labarai masu alaka:

Hotunan fitsara: Rahma Sadau ta ce ita ba ‘yar Kano ba ce- Kannywood

Jaruma Hadiza Gabon

Hadiza Gabon: ita ce ta biyu wajen yawan mabiya a shafin Instagram inda take da yawan mabiya har kimanin miliyan daya da dubu dari biyar.

Rikicin Hadiza Gabon da jaruma Amina Amal shi ne ya kara yayata Hadiza Gabon a shekarar 2019.

Jaruma Nafisa Abdullahi

Nafisa Abdullahi: tana da yawan mabiya har miliyan daya da dubu dari uku.

Jarumi Ali Nuhu

Ali Nuhu: Wanda ake yiwa lakabi da sarkin Kannywood yana da mabiya har miliyan daya da dubu dari uku.

Labarai masu alaka:

Ni da Ali Nuhu laifunmu ne ke haifar da matsala a Kannywood –Adam Zango

Jarumi Adam A. Zango

Adam A. Zango: shi ke marawa Ali Nuhu baya wanda yake da mabiya miliyan daya da dubu dari biyu a dandalin na Instagram, a wannan shekarar da muke bankwana da ita dai an ta faman tafka dambarwa tsakanin Ali Nuhu da Adam Zango wadda har ta kaisu gaban kotu, kafin daga bisani dattawan Kannywood su samar da maslaha a tsakaninsu.

A yanzu haka dai tuni Adam Zango ya ce ya fice daga masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood sannan yayi hijira daga jihar Kano, inda ya koma jihar Legas da zama.

Kazalika a kwanakin baya anyi ta cece kuce kan batun daliban da Adam A. Zango yace ya dauki nauyin karatunsu a wata makaranta dake Zariya.

Labarai masu alaka:

Da gaske Adam Zango ya dauki nauyin karatun dalibai?

Jaruma Fati Washa

Fati Washa: Itama tana da mabiya har miliyan daya da dubu dari biyu a dandalin Instagram, a kwanakin baya ne dai akayi ta cece kuce a kafafan sada zumunta kan wasu hotuna da ta wallafa a shafinta na Instagram.

Kazalika a shekarar da muke bankwana da ita ne aka karrama Fati Washa da lambar yabo ta gwarzuwar Kannywood a wani taron baje kolin fina-finai da akayi a Birtaniya.

Sai dai shi ma cece kuce ya biyo baya sakamakon wani hotonsu da jaruma Rahma Sadau ta wallafa a shafin Twitter.

Jaruma Maryam Booth

Maryam Booth: Itama tana da mabiyar har miliyan daya da dubu dari biyu a dandalin Instagram.

Jaruma Hafsat Idris

Hafsat Idris: Wadda akafi sani da Barauniya tana da mabiya har miliyan daya da dubu dari biyu.

A farkon watan Disambar da muke ciki ne aka yita cece kuce kan wani hoto da jaruma Hafsat Idris ta wallafa da mahaifinta bayan da Allah yayi masa rasuwa, inda jama’a suka rika cewa ta dauki hoton bayan da ya rasu zargin da ta musanta inda ta ce sun dauki hoton ne tun yana da ransa.

Labari masu alaka:

Ban dauki “selfie” da gawar mahaifina ba -Hafsat Idris

Jarumi Sadiq Sani Sadiq

Sadiq Sani Sadiq: Jarumin da yayi fice wajen fitowa a kowane irin mataki a shirin Film yana da mabiya har miliyan guda.

Jaruma Maryam Yahya

Maryam Yahya: Matashiyar Jarumar da tauraruwarta tafi haskawa a shekarar 2019 tana da mabiya har miliyan guda.

Jama’a na kallon cewa shigowar Maryam Yahya masana’antar ya haifar da karin shigowar kananan yara domin a dama dasu a harkar fina-finan Hausa.

Kazalika ita ma Maryam Yahaya ta haifar da cece kuce akanta a kafafan sada zumunta tun daga batun haduwarta da dan kwallon kafar nan Pogba a kasar Saudia, da kuma wani bidiyonta da aka dauka ba tare da ta sani ba, aka kuma rika yadawa a kafafan sada zumunta.

Labarai masu alaka:

Kun san abinda ya hana jaruma Maryam Yahya aure?

Na taba yin soyayya da Maryam Yahaya a baya –Mai Shadda

Jaruma Aysha Humair

Aysha Humaira: Tayi fice a dandalin sada zumunta na Instagram kafin daga bisani a fara ganinta a fina-finan Hausa, yanzu haka tana da mabiya har miliyan guda a dandalin na Instagram.

KannyWood

Naziru ya yi Murabus daga Sarkin Wakar Sarkin Kano

Published

on

Fitaccen mawakin Hausar nan, Nazir M. Ahmad, yayi murabus daga sarautar sa ta Sarkin Wakar Sarkin Kano.

Cikin wata sanarwa da Nazirun ya sanyawa hannu mai dauke da kwanan watan ranar 13, ga watan Maris din da muke ciki, Naziru ya ce ya ajiye sarautar nan take.
Sannan yayi godiya ga masarautar Kano bisa bashi wannan sarauta da ya shafe shekara guda akan ta.

Idan zaku iya tunawa dai a watan Disamba na shekarar 2018 ne, Sarkin Kano na wancan lokacin Muhammadu Sanusi II ya nada Nazir M. Ahmad matsayin Sarkin Wakar Sarkin Kano.

Naziru M. Ahmd yayi suna wajen wakar sarakuna.

Wakar sa mai farin jini da ya yiwa Sarkin Kanon na wancan lokaci ita ce “Mata ku dau turame” wadda har yanzu jama’a ke cigaba da yayin ta, ta yadda akan sanya wakar a mafi yawan bukukuwa da ake gudanarwa a kasar Hausa, kamar yadda wani rahoton BBC Hausa ya bayyana a makon da ya gabata.

Continue Reading

KannyWood

Yanzu-yanzu: Mahaifin Umar M. Sheriff ya rasu

Published

on

Rahotonni daga jihar Kaduna na cewa Allah ya yiwa Malam Sheriff Muhammad rasuwa a daren Litinin dinnan.

Marigayin mahaifi ne ga fitaccen mawakin Hausar nan Umar M. Sheriff da kuma jarumai a masana’antar fina-finan Hausa Abdul, da Umar M. Sheriff.

Daya daga cikin makusantan Umar M. Sheriff a masana’antar Kannywood Kuma fitaccen mai shirya fina-finan Hausa Abubakar Bashir Mai Shadda shi ne ya tabbatarwa da Freedom Radio wannan rasuwa.

Za ayi jana’izar marigayin a gobe Talata idan Allah ya kaimu, a gidan marigayin dake ‘Yan Kifi a Rigasa ta jihar Kaduna.

Muna fatan Allah ya gafarta masa, ya sanya aljannah makoma Amin.

Continue Reading

KannyWood

Addu’o’I sun fara nasara a Kannywood

Published

on

Gamayyar masu shirya fina-finan Hausa sunyi wani zaman na musamman don kawo gyara a masana’antar.

Zaman wanda ya gudana a ranar alhamis din da ta gabata, ya hadar da kungiyar masu shirya fina-finan hausa ta kasa wato MOPPON karkashin jagorancin shugabanta Dakta Ahmad Sarari.

Sai kuma dattawan kungiyar Arewa Film Makers Association of Nigeria.

Wannan taro dai ya biyo bayan addu’o’in da azumi da ‘yan masana’antar suka fara a makon da ya gabata.

Da yake jawabi jim kadan bayan kammala taron shugaban kungiyar MOPPON Dakta Ahmad Sarari ya ce sun cimma matsaya ta tabbatar da hadin kai a tsakanin ‘ya’yan masana’antar domin ciyar da sana’ar gaba.

Karin labarai:

Halin da ake ciki a Kannywood a wannan mako

Kun san jaruman da sukafi yawan mabiya a Kannywood?

Ita ma a nata bangaren Rashida Adamu Mai Sa’a ta bayyana cewa babban abinda suka a gaba shi ne ciyar da masana’antar gaba, domin basu da abinda yafi masana’antar.

Taron ya samu halartar sakataren kungiyar ta MOPPON Salisu Officer da kuma Sani Sule da Rashida Adamu Abdullahi Mai sa’a daga kungiyar Arewa Film Makers.

Sai kuma Kabiru Mai Kaba, shugaban kungiyar MOPPON ta jihar Kano, da kuma Jamilu Yakasai shugaban kungiyar Arewa Film Makers na jihar Kano.

Yanzu haka dai tuni gamayyar kungiyoyin suka hallara a jihar Kaduna domin cigaba da gabatar da addu’o’I a yau Asabar.

Continue Reading

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 324,396 other subscribers.

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!