Labarai
Kungiyar agajin gaggawa ta red cross ta musanta hallaka ma’aikatanta
Kungiyar bada agajin gaggawa ta red cross ta musanta rahotannin da ke cewar mayakan boko harmam sun hallaka ma’aikatanta.
A ranar Alhamis ne mayakan boko Haram su ka kai hari a kauyen Rann da ke jihar Borno inda suka hallaka mutane da dama.
Rahotanni dai sun nuna cewar yayin harin an kashe ma’aikatan majalisar dinkin duniya guda uku da kuma sojojin kasar nan guda takwas, inda kuma Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewar an kashe jami’in kungiyar guda daya.
Sai dai kungiyar bada agajin gaggawa ta ICRC ta fitar da wani rubutu ta shafin ta na internet inda ta musanta wancan rahoton na NAN din, inda kuma ta zargi Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN da sanya wasu kafafen yada labaran da yada labaran da ba haka ya ke ba.
Hukumar dai ta ICRC a Najeriya na aikin rabon abinci ne a sansanin yan gudun hijirar da ke Rann a lokacin da aka kai harin amma babu wanda ya mutu a cikin ma’aikatan ta a cewar jami’in yada labaran kungiyar Matijevic Mosimann.
Ya kuma ce dukkanin ma’aikatan kungiyar da ke aikin sa kai da suke a wurin lokacin da harin ya faru sunanan cikin koshin lafiya kuma ba wanda ya cutu.